Talla

Yan Wasan Super Eagles na Najeriya sun ci Jamhuriyar Afirka 2 babu ko ɗaya

10 Oktoba, 2021
ABUJA, NIJERIYA - Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ta yi rashin nasara a hannun Super Eagles da ci 2-0 a karawar da suka yi a Kamaru ranar Lahadi.

Yan Wasan sun buga wasanni na huɗu a rukuni na uku a fafatawar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a shekarar 2022.

Najeria ta ci kwallon biyu ta hannun Leon Balogun da kuma abokinsa Victor Osimhen.

Da wannan sakamokon Super Eagles ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburi da maki tara, bayan buga wasa huɗu a rukuni na uku.

Jamhuriyar Afirka tana da maki huɗu a wasa huɗu da ta buga, wanda anjima ne Cape Verde mai maki huɗu a wasa uku za ta karɓi bakuncin Liberia mai maki itama uku a karawa uku da ta yi a rukuni na uku.

Ranar Alhamis Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ta je ta doke Najeriya 1-0 da suka fafata a filin wasa na Teslim Balogun da ke jihar Legas, Najeriya

Jamhuriyar Afirka ta ci kwallon ne daf da za a tashi daga karawar ta hannun Karl Namnganda.

Cape Verde ta je ta ci Liberia 2-1 a fafatawa ta uku ta cikin rukuni na ukun ranar Alhamis.

Tun kan buga wasa na uku kocin Najeriya, Genot Rohr ya sanar da 'yan kwallon da za su buga masa fafata biyu da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, wadda take wasanninta a Kamaru a matsayin gida.

Ko kun san 'Yan wasan Super Eagles:

Masu tsaron raga su ne: Francis Uzoho (AC Omonia, Cyprus); Daniel Akpeyi (Kaizer Chiefs, South Africa); Maduka Okoye (Sparta Rotterdam, The Netherlands

Masu tsaron baya su ne: Chidozie Awaziem (Alanyaspor FC, Turkey); Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain); Leon Balogun (Glasgow Rangers, Scotland); William Ekong (Watford FC, England); Olaoluwa Aina (Torino FC, Italy); Jamilu Collins (SC Padeborn 07, Germany); Abdullahi Shehu (AC Omonia, Cyprus); Calvin Ughelumba (Glasgow Rangers, Scotland); Kevin Akpoguma (TSG Hoffenheim, Germany)

Masu buga tsakiya su ne: Frank Onyeka (Brentford FC, England); Joseph Ayodele-Aribo (Galsgow Rangers, Scotland); Innocent Bonke (Malmo FF, Sweden); Alex Iwobi (Everton FC, England); Kelechi Iheanacho (Leicester City, England)

Masu cin kwallo su ne: Ahmed Musa (Fatih Karagumruk, Turkey); Samuel Kalu (FC Bordeaux, France); Victor Osimhen (Napoli FC, Italy); Moses Simon (FC Nantes, France); Paul Onuachu (KRC Genk, Belgium); Chidera Ejuke (CSKA Moscow, Russia)

Post a Comment

0 Comments