Talla

Wasu Ƴan Bindiga Sun Fatattaki Ƴansanda a Caji Ofis

11 Oktoba  2021

ADAMAWA, NIJERIYA - Wasu ƴan bindiga sun shiga wani ofishin Ƴansanda suka buɗe wuta wanda ya sa ƴansandan dake aiki a wannnan ranar guduwa daga ofishin, masu garkuwar sun yi awon gaba da wata mace da ɗanta dake caji ofis ɗin.

Daga nan kuma maharan sai suka shiga wani gida suka sake yin garkuwa da wata mata da ƴarta. Bayan sun yi nisa sai suka sake shawara sannan suka saki sauran mutanen amma sun tafi da uwar da ɗiyarta waɗanda suke cikin alhinin rashin mahaifinsu.

Maharan sun shiga caji ofis ɗin ne da misalin ƙarfe ɗaya da rabi na rana.

Rahotanni sun ce maharan dai sau uku suna shiga gidan mamacin tare da yin garkuwa da mutanen gidan. Ko kafin maigidan ya rasu, sai da mahara suka yi garkuwa da shi sau biyu. Bayan kuma ya rasu sai da maharan suka ƴara shiga gidan suka yi garkuwa da mutanen gidan.

Mai magana da yawun rundunar ƴansanda na Jihar Adamawa, DSP Suleiman Yahaya Guroji ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya kuma bayyana cewa maharan sun raba kansu ne wasu suka kai hari a caji ofis na ƴansanda suka tarwatsa su, sannan sauran maharan suka shiga gidan marigayin suka yi garkuwa da uwargidansa da ɗiyarsa.

Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na daga cikin garuruwan da mahara suka addaba.

Wannan da ma wasu labarai, ku biyo mu a shafin www.arewanews.org.ng

Post a Comment

0 Comments