Umar M Shareef: Waƙar Fanan Download Fanan Song here
Amshi Namiji
Fanan,
Ƙaunarki cikin zuciya,
Ki ban, soyayya na zo ki ban.
Amshi Macce
Fanan,
Farin cikin zuciyaa ta,
Kai ka ban, Soyayyata
kai ne ka ban.
Baiti Namiji
Na baki kai na tuni,
Duk yadda za ki yi da ni,
A gunki bana gani,
Aibu.
Gare ni ke magani,
Sila ta warkar dani,
Allahu ne massani,
Gaibu
Ga wata baƙuwa,
Wacce zan ba ruwa,
Ke kaɗai ce ƙawa,
Ƴar'uwa, masoyiya,
mai ciran damuwa,
Amshi Namiji
Fanan,
Ƙaunarki cikin zuciya,
Ki ban, soyayya na zo ki ban.
Kiɗa...
Baiti Macce
Tun da kai na sa gaba,
Bani babu fargaba,
Yaƙi ba zai cini ba,
Ba zan guje ka ba,
Don ban gano kamar ka ba,
Koda akwai baza ni je ba.
Amshi Macce
Fanan,
Farin cikin zuciyaa ta,
Kai ka ban, Soyayyata
kai ne ka ban.
Kiɗa...
Fanan, fanan, fanan, fanan, fanan fanan fanan...
Baiti Namiji
Zani dake ko a ina,
a ganni da kee ba magana,
Hirar da mu kee in na tuna,
Sai in ji naa fara tsuma,
Domin kyan halinki,
Domin kyan surarki,
Domin kyan tafiyarki,
Kyan fuskarki,
Na daɗa sonki.
Ƴata albarka ce,
Cikin dubu na tantance,
samunki babbar sa'a ce,
Mata Kauce-kaunce.
Amshi Macce
Fanan,
Farin cikin zuciyaa ta,
Kai ka ban, Soyayyata
kai ne ka ban.
Baiti Macce
Wacce za ta kai ya ni,
Masoyina na ji da ni,
Kowa ya ganni zai sani,
Ina cikin farin ciki.
Allahu ne gwanin sani,
Cutar da babu magani,
Babu babba ba ƙanƙani,
Soyayya ina ciki.
So mara ba,
Hau kujera,
kai na zaɓa,
Zani aura,
Zan yi gaba,
babu kara,
wanda yacce,
zai taɓa ka.
Amshi Namiji
Fanan,
Ƙaunarki cikin zuciya,
Ki ban, soyayya na zo ki ban.
Fanan, fanan, fanan, fanan, fanan fanan fanan...
Fanan, fanan, fanan, fanan, fanan fanan fanan...
0 Comments