Talla

An Kashe Sabon Shugaban ISWAP Malam Baƙo

22 Oktoba, 2021

BORNO, NIJERIYA - Gwamnatin Najeriya ta sanar da kashe Malam Bako wanda ya gaji shugaban ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta ISWAP.

Babagana Monguno mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro ne ya shi ne ya bayyana haka a ranar Alhamis lokacin da yake yi wa manema labarai ƙarin bayani game da taron da suka yi da Shugaba Buhari.

A farkon watan nan ne Hafsan Hafsoshin Tsaron Nijeriya Janar Lucky Irabor ya ce,
 
"Dakarun sojojin Nijeriya sun yi nasarar kashe shugaban ƙungiyar Abu Musab Al-Barnawi.

Ya ƙara da cewa,
"Maganar gaskiya ita ce, dakarun sojan ƙasa sun yi kyakkyawan aiki saboda a cikin wata ɗaya mun yi nasarar tarwatsa shugabancin ISWAP - wato Abu Musab Al-Barnawi,"

Ya ci gaba da cewa,

"Kwana biyu da suka wuce, mutumin da ya gaje shi mai suna Malam Bako, ɗaya daga cikin mambobin Majalisar Shura na ISWAP, shi ma an kashe shi."

Yanzu ƙungiyar ba tayi ƙarin bayani ba game da kisan sabon shugaban nata, kodayake ta nuna alamun da gaske an kashe Al-Barnawi.

Post a Comment

0 Comments