Talla

Mata da Yara sun toshe babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto

20 Oktoba, 2021
ZAMFARA, NIJERIYA - Wasu mata masu zanga-zangar nuna fushinsu a kan halin ƙunci da suka shiga sun toshe hanyar Gusau zuwa Zamfara.

Wasu rahotanni a Zamfara a Arewacin Nijeriya sun tabbatar da ce, ɗaruruwan mata sun fito saman babbar hanyar zuwa Gusau da Sokoto domin nuna fushi kan halin da suke ciki na hare-haren ƴan bindiga masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.
An ga wasu hotuna da suka nuna mata na ɗauke da kaya suna tafiya bisa hanya gab da shiga garin Tsafe.

Mutanen garin waɗanda mafi yawansu mata ne da yara sun tare babbar hanyar ranar Laraba inda suka haddasa cunkoson ababen hawa.

Wani ganau ya ce, matan sun tsere wa hare-haren ƴan bindiga ne da suka addabe su, suna masu fyade. Matan sun toshe hanyar ne domin janyo hankalin gwamnati kan halin da suke ciki.
Wani direban mota a babbar tashar Gusau ya ce an shafe awanni babu wani direban da ya shigo tashar daga hanyar Funtua.

Garuruwan Zamfara da Sokoto da Kebbi da Katsina da Kaduna dai na fama da hare-haren ƴan bingida masu sace mutane don karɓar kuɗin fansa. Ko a watan daya gabata, an daɗe layukan sadarwa da hana cin kasuwanni da hana sayar da mai a jarkuna don a samu damar daƙile sace-sacen mutane.

Post a Comment

0 Comments