11 Oktoba, 2021
ABUJA, NIJERIYA — Tun tana ƙarama take fatan samun saussauƙar mutuwa wace ba sai
ta yi jinya ba. Kodayake saura ƙiris gurinta ya cika a jiya ranar lahadi 10 ga
watan Oktoba 2021 da misalin ƙarfe takwas ne tasa ran mutuwa.
Ranar asabar, tana cike da farin
ciki tare da annashuwa na cikar gurinta wato ta samu sassauƙar hanyar mutuwa. A
ranar jajibirin mutuwarta ne, tana cike da farin ciki da murmushi tare da ɗaukar
hotuna, sannan ta sha giya ta kuma ci wani samfurin abinci wanda tafi so mai
suna Medellin, cike da yaƙinin cewa gobe ne zata mutu.
Martha mace ce mai son mutane da
son nishaɗi da murmushi mai biyayya ga cocin katolika, tana da riƙon addini, ta
ɗauka cewa ita mace ce mai sa’a da nuna soyayya ga mahallicinta wanda yake
sonta kuma ya bata damar zaɓar ranar da take son mutuwa.
Tana zaune tare da ɗanta mai suna
Federico Redondo Sepulveda a Ƙasar Colombia, ƙasar da aka halasta mutuwa ta
hanyar yin allura idan mutum na fama da wata matsananciyar cuta mai wahalarwa
wadda ba a warkewa. A shekarar 1997 aka halasta dokar yin euthanasia wato
mutuwa bisa wasu dokoki amma sai a shekarar 2015 ne ta zama cikakkiyar doka.
A kan Martha ne aka fara ba da
damar yin euthanasia ga maras sa lafiya. An gano Martha na ɗauke da cutar
myotophic lateral sclerosis a shekarar 2018 cutar da ta shafi jijiyoyi sai
rayuwarta ta zama cikin azaba da wahala.
Mace ce marar tsoron mutuwa, haka
kuma bata son ta mutu bisa gado, sai ta zaɓi a ɗauki ranta kafin ciwon ya ta’azzara.
Ta fara tuntuɓar ɗanta da shawarar ɗaukar ranta, daga farko bai aminta ba, amma
daga bisani da ya lura cewa wannan ne zaɓin rayuwarta, kuma bata so ta ci gaba
da rayuwa cikin wahala, sai ya amince da zaɓinta.
Ta kasance cikin farin ciki da
annashuwa da natsuwa saboda gobe ne zata mutu, ta yi barci mai daɗi, sannan ta
ci abinci ta yi fira ta nishaɗi da ɗanta, tana da tabbacin cewa gobe ne za ta
mutu.
A ranar da zata mutu, bayan an
tura ta bisa gadon maras sa lafiya zuwa ɗakin da za ayi mata allurar, wadda
za ta saka ta barci, a hankali har ranta ya fita. A gefe ɗaya kuma, danginta da
ɗanta suna cike da alhinin rashinta, inda aka shirya bikin yin zana’idarta, da
yakinin cewa za a fiddo gawarta a ranar lahadi. Da zaran an fiddo gawarta ne za
a yi bikin mutuwarta sannan a ƙona gawar a kuma binne ta.
Amma wani abun da bata sani ba,
Allah SWA ne kawai ya san ranar mutuwar kowa, bayan an shiga da ita ɗakin maras
sa lafiya, sai asibitin ta fito da wasu takardu waɗanda suka ƙi yadda da ɗaukar
ranta a daidai lokacin da take so. Asibitin ta ce ba ta cika ka’idojin mutuwa a
wannan lokaci ba.
Wannan da ma wasu labarai ku biyo
mu a shafin www.arewanews.org.ng
0 Comments