22 Oktoba, 2021
ABUJA, NIJERIYA - Abubakar Malami wato Ministan Shari’a ya ce, rahoton kwamitin da ofishinsa ya kafa ya yi faɗi cewa, shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya yi ta harzuƙa magoya bayansa ta hanyar amfani da kafar rediyo taBiafra wadda aka ƙirƙira a yanar gizo.
Malami ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudana a ma’aikatar shari’a dake birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a inda ya ce kiran da Kanu ya yiwa magoya bayansa ya haddasa asarar rayuka da dukoyin al'umma kuma ya haddasa ɗar-ɗar a zukatan mazauna yanki Igbo.
Ya ƙara da cewa,
Nnamdi Kanu ya kuma yi amfani da zanga-zangar Endsars da ta rikiɗe zuwa tarzoma wajen ingiza mutane har aka rasa dimbin rayuka da dukiyoyi.
Malami ya ce, a tsakanin jami’an tsaro an samu asarar rayukan mutane 175 da suka haɗa da ƴansanda 128, sojoji 37, sauran ma’aikatan tsaro 10 sakamakon harzuka magoya bayansa da Nnamdi Kanu ya yi.
Daga cikin waɗanda suka rasa ransu akwai: basarake Obi Nwanyi na al’umman Okudo, Basarake Eze E. Anyaochukwu, da Basarake Eze Samson Osonuwa na al’umman Ehiebene na Owerri, da mijin marigayiya tsohuwar babbar darakatar hukumar NAFDAC Dora Akunyili da dai sauransu.
A ranar Alhamis Kanu ya sake bayyana a gaban kotun tarayya da ke Abuja a ci gaba da sauraren shari'ar da ake masa inda ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.
Har yanzu dai gidan radiyon tasa na yaɗa shirye-shirye a yanar gizo inda ake amfani fa kafar sadarwa da Fesbuk fa Youtube wajen yaɗa shirye-shiryen ƴan awaren Biafra.
0 Comments