24 Oktoba, 2021
Gaga Malam Nura A Yar'adua Assalafy
Slm,
Yana cikin matsalar da mata suke kokawa da ita ga mazajensu, ita ce saurin fitar da maniyyi a lokacin saduwar aure, tun kafin su samu gamsuwa. Kuma su ma maza da yawa suna fama da wannan matsalar, kuma tana damun su! To insha Allah ga mafita:-
Ma'anarsa:-
Shi ne namiji ya yi saurin inzali a cikin kasa da minti biyu. In ko ya kai minti biyu abin da ya yi sama, kuma gabansa bai kwanta ba da karfinsa, toh lafiyarshi lau.
Sabubbansa:-
1. Halitta da dabi'a:-
Akwai wanda haka Allah Ta'ala ya halicce shi da shi.
2. Shekaru
3. Stress
4. Diabetes
5. Ciwon sanyi
6. Dankanoma/Basur
7. Yin masturbation tun kafin aure
8. Yawan Shan ruwan sanyi da kayan zaki.
Mafita:-
1. Exercise
2. Daidaita abinci:-
A. Cin ganyayyaki
B. Rage Shan zaki da maiko da Kishi 50% ko sama da hakan.
C. Amfani da tafarnuwa
D. Speed Technique:- shi ne idan miji yana cikin saduwa, sai ya ji maniyyi zai fito, toh sai ya tsaya ko ya zare al'aurarsa, har zuwa dan lokacin da maniyyi zai koma, sannan sai ya cigaba... Duk sadda ya ji hakan sai ya kara zarewa. Toh yau da gobe jijiyarsa za ta saba har ya daidaita.
E. Masturbation/Istimna'i:- shi ne matar ta yi ma mijin wasa da gabansa har ya fitar da maniyyi. Toh Kamar bayan mintuna sai su yi kwanciyar aure. Toh insha Allah zai jima sosai a wannan saduwar.
F. More than One Round:- shi ne mijin ya kara zagaye na biyu bayan na farkon da aka yi cikin sauri, lallai tabbas zai jima a zagaye na biyun fiye da na farko.
G. Long Romancing/Dogon wasanni:- shi ne miji ya dauki lokaci mai tsawo a wajen wasa da iyali kafin shiga cikin jikinta da saduwa. Hakan zai fi saurin gamsar da matar.
Magani
1. 'Ya'yan kabewa da Madara:- shi ne a samu 'ya'yan kabewa busassu a dake su.. Toh garin sai a dunga damawa da madara ana sha safe da yamma. Har zuwa lokacin da zai daidaita.
2. Lemun tsami, Zuma da citta:- Shi ne a samu lemun tsami masu ruwa kamar guda 7-10 sai a matse ruwan, sai garin citta babban cokali 5, sai zuma kamar robar yogurt. A hade su guri daya. Sai ya dunga sha cokali biyu:- safe, rana da dare. Har tsawon lokacin da zai daidaita.
3. Bawon Kankana, tsamiya, tafarnuwa da ruwa:- shi ne ayi blending din su a guri daya. Sai ya dunga sha rabin kofi:- safe kafin ayi kalaci da minti 30 ko fiye, da kuma idan za a kwanta bacci da daddare. Har zuwa lokacin da zai daidaita.
Kyakkyawan Fata:-
Insha Allah idan aka kiyaye wadannan shawarwari, toh miji zai koma normal da izinin Allah (Musamman ba natural matsala ba ce)
Chairman Al-Mu'asharah
(Kingiyar wayar da kai da gyara zamantakewar aure, Katsina)
Nura A Yar'adua Assalafy
Gmail:- [email protected]
09031599997
0 Comments