Can
wani zamani da ya gaba ta, Kasuwar Katsina ita ce babbar kasuwa a duk faɗin Ƙasar Hausa. Mutane daga ƙasashe daban-daban suna zuwa cin
kasuwa.
An yi wani Dattijo mai tarin dukiya ga tausayin mutane da taimakon
talakawa, kullum za a iske shi zaune bisa kujera a zauren gidansa, tare da wani
bawansa ya zauna ƙasa suna fira. Har ƙasashen Larabawa yake zuwa yin
fatauci irinsu Saudiya da Sudan, duk kuwa lokacin da ya yi aniyar fita fatauci
ayari da dama kan bisa su damƙa masa amanar dukiyarsu saboda riƙon amanarsa.
Babbar ɗabi’arsa ita ce, son dabbobi, duk inda za shi dabbobi ne abokan
rakiyarsa, duk kuwa abin da ya ci sai ya ba dabbobinsa irinsa. Akwai wata
barewa da yake tsananin so a cikin dabbobinsa.
Wata rana Dattijo ya shirya ya yi aniyar
tafiya Sudan yin fatauci, ya shirya raƙumansa da alfadarai, ya ɗora masu kaya niƙi-niƙi,
ya gama shiri ya hau wata amintacciyar goɗiyarsa. Bayan La’asar ya fita ta ƙofar
Sauri don neman sa’a. Bakin ƙofa ya haɗu da wani Saurayi haye bisa dokinsa
danda riƙe da keji guda biyu, ɗaya ɓera ke cikinsa ɗaya kuwa mage ce
cikinsa.
Su ka yi gaisuwa sannan suka yi gaba, suka
sake haɗuwa da wata Budurwa, tana sanye da wani farin mayafi, ta yi masu
sallama sannan ta tambayi shugaban ayari, Dattijon ya karɓe ta cikin aminci,
suka yi gaba tare.
Suna cikin tafiya sun keta sahara ta
farko, sun shiga wata sarƙaƙiyar daji, suka samu waje suka yada zango ƙarƙashin
wata itaciya. Madugu ya fiddo gurasa da zumuwa suka ci su ka yi ibadarsu sannan
suka sake nausawa cikin daji suna ta addu’o’i. Suna cikin tafiya ‘yan fashi
suka tare su, suna riƙe da muggan makamai sai mazurai suke yi, aka ja Datijjo,
da saurayi da budurwa zuwa gaban sarkin ɓarayin, aka ɗaure su sannan aka duƙar
da su gaban sarkin ɓarayi.
Ya harare su ya ce masu; “Ku ne ku ka sace
mani dukiya?”
Dattijo
ya ce, “Ba mu yashe maka dukiya ba.”
Sarkin Ɓarayi
ya ce, “Ta cikin saharar da ku ka biyo na aje dukiyata, in kuwa ba ku fiddo ta
ba sai na fille maku kawuna, ke kuwa ki zama matar Sarkin Ɓarayi”
Sarkin ɓarayi
ya kalli Dattijo ya ce, “Za ka iya ceton ranka da hikaya?”
Dattijo ya yi nutso cikin tunani sannan ya
fara ba da labari da cewa.[1]
Tambayoyi:
1. A
wancan zamanin, wace kasuwa ce babbar kasuwa a ƙasar Hausa?
2. Wane
dalili yasa kasuwar garin Katsina ta zama babbar kasuwa?
3. Lisaffa ƙabilun
da ke zuwa cin kasuwa a ƙasar Katsina?
4. Yi
taƙaitaccen jawabi kan halayyar wannan dattijo?
5. Cike
waɗannan guraben:
6. Bayan
la’asar ya fita ta _____________ don neman sa’a.
7. Saurayi
haye bisa _______ riƙe da _________________.
8. ___________
ya fiddo __________ da zumuwa suka ci.
9. Suna
cikin tafiya sun keta ________ ta farko.
10. Ya
harare su ya ce masu; “________________________?”
1. An ciro wannan labari mai suna ‘Labarin Dattijo, Saurayi da
Budurwa’ daga littafin ‘Hikimarka Jarinka’ Littafi na Biyu wanda Bello Hamisu
Ida ya rubuta
0 Comments