Talla

Labarai uku da suka cancaci lashe Gasar Hikayata ta 2021

27 Oktoba, 2021
Labarai Uku da suka cancanci lashe gasar Hikayata

Labarin Ramat

Labari ne kan wata mata mai suna Ramat da ta shiga aikin ƴan sanda a ƙasar Hausa kuma ta haɗu da mijinta a bakin aiki wanda shi ma ɗan sanda ne.

Sun yi aure sun shimfiɗa rayuwa mai kyau mai cike da albarka kuma sun samu rabon ɗa ɗaya tal.

Sun nuna wa ɗan nasu gata har girmansa inda suka kai shi Turai karatu sai dai dawowarsa ke da wuya ya aikata wani mummunan laifi wanda ya jefa iyayensa cikin matsanancin hali.

Ramat ta shiga halin gaba kura baya sayaki - wato ta kuɓutar da ɗanta ko ta riƙe martabar aikinta na babbar jami'ar ƴan sanda.

Daga ƙarshe ta ɗauki matakin da ya mai karatu ba zai taɓa tsammani ba sai dai labarin ya yi kyakkayawan ƙarshe don kuwa an samu mafita.

Labarin Haƙƙina

Wannan labari ne mai sosa rai a kan wata budurwa da ta fuskanci babban ƙalubale na rayuwa.

Inda take tunanin za ta ɗan ji sanyi sai ta fuskanci ƙuna, ta shiga halin ha'ula'i.

Labarin Haƙƙina ya taɓo jigo na fyaɗe da tsoron tsangwama da wahalhalun gidan aure da rashin girmama ƴa mace.

Marubuciyar wannan labarin ta yi amfani da wani salo na rubutu inda ta bai wa tauraruwar labarin hanyar sama wa kanta mafita duk da matsanancin halin da take ciki.


Labarin Butulci

Labarin Butulci labari ne kan wata mata da ƙaddara ta faɗa mata aka yi garkuwa da ita, ga shi tana da ƙaramin ciki.

Tana hannun masu garkuwa tana cike da fargaba da zaƙuwar ta sanar da mijinta samun cikin nata.

Bayan ta kuɓuto daga hannun masu garkuwa da mutane ta isa gida a wahalce, saidai ba ta samu bayyana wa maigidan nata kyakkayawan fatan da take rawar ƙafar sanar da shi ba saboda wani mummunan labari da ta gamu da shi.

Post a Comment

0 Comments