Marigayi Malam Adam malami ne ɗan asalin garin Koza gake ƙaramar hukumar Mai'adua. A zamanin rayuwarsa, mutum ne mai son mutane da kunya da kawaici da girmama al'umma da kuma nuna ƙauna da soyayya ga addininsa. Ya kan yi murna a duk irin wannan wata na Maulud don nuna ƙaunarsa ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).
Ga hotunan wasu daga cikin zuri'arsa suna mana barka da Maulud:
Mallam Mannir, Malami ne kuma limami wanda ke gabatar da karatuttuka a Masallatai da majalisu na da'awa.
Da kuma Hafiz Adam Koza masani a fannin harshen Hausa, ɗalibi, malami kuma sha'iri wanda ya shahara ta ɓangarori da dama.
Da sauran Zuri'arsa da abokai da aminai da ƴan'uwa suna farin ciki da wannan wata mai albarka wanda aka haifi fiyayyen hallita Annabinmu, ma'aiki wanda aka yi duniya da lahira dominsa.
Muna fata kuma muna roƙo Allah ya ƙara albarka da ɗaukaka a cikin wannan zuri'a ta Malam Adam Koza (Marigayi). Allah ya jiƙansa da rahma ya ƙautata makwancinsa albarkacin Annabi Muhammadu Rasulullah.
0 Comments