10
Oktoba, 2021
ABUJA, NIJERIYA — Wani abin alfahari ne mahaifa su tarbiyatar da ɗa ko ɗiyarsu wanda za su
zama sadaƙa gare su da al’umma da addini. Kodayake, bikukuwa sun zama wani abin
alfahari da birgewar da nishaɗi, amma ga Habiba abin ba haka yake ba.
Duk da yake bikin
zagayowar Haihuwa ya zama wani abin al’ada a yanzu, amma Ummin babba bikin
zagayowar cikar shekarunta ya zamar mata wata rana ta tunawa da mahaifinta tare
da yi masa addu’o’in samun rahma.
Haka kuma, ranar ta
zama ranar tunawa da ‘yanuwanta da take ƙauna waɗanda suka zamar mata bangon
data jingina da su.
Habiba yarinya ce mai
tarbiya da girmama na gaba, da biyayya da hangen nesa, da hankali da son
nishaɗi, da fara’a da son mutane. Tsohuwar ɗaliba ce a Makarantar Jeka ka dawo
dake Barikin Sojoji ta Katsina da aka fi sani da Natsinta, kuma ita ce shugabar
ɗalibai ta mata waɗanda suka kamala a shekarar 2020.
Hazaƙarta da maida
hankali wajen karatu yasa ta samu wannan muƙami, bayan wannan kuma tasha samun
wasu muƙamai a ciki da wajen makaranta. Ta taɓa shiga gasar Hikayata ta mata
wadda BBC Hausa ke shiryawa duk shekara a shekarar 2021. Bayan wannan gasa
tasha shiga gasa don nuna fikirarta da hikimarta da zurfin tunaninta wajen
hanken nesa.
Haziƙar, Habiba tafi
so a kira ta da sunanan ‘Ummin Baba’ don nuna soyuwarta ga zuri’arta. Tana
tsananin kulawa da ƙawarta mai suna Ruƙayya wadda ta zama aminiyarta kuma
yar’uwa. Ƙawayenta kuwa su ne, Salma da Rahma da Amira da Humaira da wasu da
dama.
Ta kan yi alhinin
ranar da ta rasa mahaifinta, (Allah ya jikansa da rahma). Haka kuma tana yawan
farin ciki a duk lokacin da ‘yanuwanta ke cikin farin ciki suna tayata murna.
Tana son cin abincin
gargajiya, tana son saka suturar gargajiya, haka kuma tana son duk kyautar da
aka yi mata wacce zata sanyata farin ciki.
A wannan rana mai
albarka, daidai wannan lokaci mai cike da farin ciki, Habiba wato Ummin Baba
tana cikin farin ciki tare da yan’uwanta da abokanta da zuri’arta da sauran
al’umma. Tana farin cikin zagayowar ranar haihuwarta tare da sauran al’umma
baki ɗaya.
1 Comments
Muna taya habiba murnar zagayowar ranar haihuwarta ,Allah yakaro wasu masu albarkah
ReplyDelete