Talla

Cutar Gudawa

Cutar gudawa wani nau’i ne da ya ke sawa ayi ta tsugunni tare da yin gudawa mai ruwa-ruwa a kalla sau huɗu ko biyar a duk rana. Wasu lokutan in cutar ta yi tsanani, a kan ɗauki kwana-da-kwanaki ana gudawa wanda ke jawo bushewar jiki saboda ƙarancin ruwa a cikin jiki, wanda hakan ke sanya wa kamanni su canza sannan fata ta tsane, haka kuma fitsari ya ragu kuma a samu ƙaruwar bugun zuciya, daga bisani kuma a kan fita daga hayyaci idan cutar ta yi tsanani. Abinda ke sa kamuwa da cutar shi ne rashin tsaftar abinci ko ruwa ko kuma yaɗuwar cutar daga wanda ya kamu.

 Cutar gudawa ta kasu kashi uku, su ne kamar haka: gudawa mai ruwa-ruwa, gudawa mai jini-jini da gudawa mai daɗewa. Gudawa mai ruwa-ruwa na iya kasancewa saboda kamuwa da cutar kwalara. Idan kuwa akwai gudawa mai jini-jini, an fi kiranta da atini.

 Gudawa ita kadai ba cuta bace amma alamace da take nuna cewa wani abu yana tafiya ba dai-dai ba a jikin ɗan-adam. Yara ƙanana musamman na goye sun fi manya shiga cikin haɗarin kamuwa da gudawa, kuma yara sukan galabaita sosai fiye da manya a duk lokacin da suka yi gudawa musamman ma idan aka yi rashin dace ta zo da amai (hararwa).

 Hanyoyin kare faruwar gudawa sun hada da: Tsaftar muhalli, ya kamata a tabbatar da tsaftar muhalli, kamar share gida da kewaye a ƙalla sau uku a rana; amfani da abun zuba shara rufaffe domin barin abun zuba shara a bude kan jawo ƙudaje da ƙadangaru a gida, kuma yara sukansa hannuwansu a ciki domin ɗaukar wani abun su yi wasa da shi;

Rufe masai da murfi a koda yaushe, nisantar da masai daga gurin dafa abinci, rijiya da sauransu; zubar da kashin yara a masai da zarar sun gama domin barinsa a buɗe a cikin gida kan jawo ƙudaje waɗanda za su ɗauki kwayoyin cuta daga kashin su sa a cikin abinci, ko ruwan sha wanda ke jawo gudawa;

Rufe randa da murfi wanda zai rufe ta, barinta a buɗe kan jawo faɗawar kwayoyin cuta cikin ruwan. Ga wanda ya kamu da gudawa ya kamata a bashi taimakon gaggawa a gida kafin a kai shi asibiti, ta hanyar bashi ruwan gishiri da sukari akai-akai.

Bincike ya nuna cewa, duk lokacin da aka fara ruwan sama wato faɗuwar damina muhalli ya kan gurɓace saboda ruwa, musamman ma wuraren da mutane suke kashi a fili, da kuma inda ake zubar da shara babu ɗaukar matakin tsaftace wajen sharar da kuma muhalli, waɗannan suna taimakawa sosai wajen yaɗuwar cutar gudawa.

Tambayoyi:

1.    Me ke jawo cutar gudawa?

2.    Cutar gudawa ta kasu kashi nawa?

3.    Gudawa alama ce ta?

4.    Lissafa matakai biyu na kariya daga cutar gudawa?

5.    Waɗanne alamomi ne ke nuna an kamu da gudawa?

6.    Cike waɗannan gurabe:

7.    Cutar gudawa wani nau’i ne da ya ke

8.    Gudawa wanda ke jawo bushewar jiki saboda ƙarancin

9.    Cutar gudawa ta kasu kashi uku, su ne kamar haka:

 

 

 

 

 


Post a Comment

0 Comments