Talla

Ana kashe Fulani Makiyaya a Kasuwar Mammande dake cikin Jihar Sokoto

 9 Oktoba, 2021



SOKOTO, NIJERIYA Fulani al’umma ce mai tarihi da silsila da usuli a Arewacin Nijeriya, har ma a kan ce Hausa-Fulani don a nuna muhimmacin al’ummar da harshen. Musamman a yankunan Sokoto da Katsina da Kano da Zamfara inda sarakunan Fulani suka yi mulki tare da kawo ci gaba a waɗannan masarautu.

Yawaitar hare-hare da tashe-tashen hankulla da kuma satar mutane don amsar kuɗin fansa ya taimaka wajen rage wa wannan ƙabila martaba a idon duniya. Wasu shuwagabannin Fulani makiyaya sun yi zargin cewa ana kaiwa Fulani harin kan mai uwa da wabi, inda ake kashe Fulani waɗanda basu ji ba, ba su gani ba a wasu sassan Jihar Sokoto.

Ɗaya daga cikin shuwagabannin Miyatti Allah wato shuwagabannin Fulani na yankin Sokoto mai suna Abubakar Umar ya koka a kan yadda ake kisan Fulani a wasu yankuna na Jihar Sokoto.

Ya yi ƙarin bayani inda ya ce,

“Yan sa kai, na  ɗaukar doka da hannunsu inda suke zuwa kasuwannin yankinsu ɗauke da bindigogi da sanduna da makamai su kama Bafillace da ya tari gabansu sannan su yi masa duka wani lokacin har da kisa”

Ya ƙara da cewa,

“An kawo masu gawar Fulani goma sha uku waɗanda aka kashe a kasuwar Mammande, haka kuma an kawo masu wasu gawarwakin da aka kashe a garin Giyawa, duka garuruwan suna cikin Jihar Sokoto”

Sarkin Fulani na Ƙaramar Hukumar Sokoto ta Kudu wato Nasiru Aliyu ya ce,

“Ba a yankin Gwadabawa wannan aika-aika ta tsaya ba, abun ya shafi hukumomin Tangaza da Gwaranyo. a waɗannan yankuna Bafillatani bashi da ikon shiga mota ko ya je kasuwa, sai a kashe shi ba tare da bincikar aikinsa ba, wasu daga cikin waɗanda ake kashewa malamai ne, duk wanda aka gani sai ayi masu kuɗin goro a ɗauka duk ɓarayi ne, wanda ba haka bane”

Ya ƙara da cewa,

“Yan sa kai ɗaukar doka kawai suke yi da hannunsu, suna kashe Fulanin da basu ji ba, basu gani ba”

Rundunar Yansanda ta Jihar Sokoto ta ce, ta samu labarin abinda ya faru a kasuwar Mammande, an yi bincike an gano waɗanda suka aikata wannan laifi, kuma an kama su ana masu bincike.

Garuruwan Sokoto, da Katsina da Zamfara da Kaduna dai na fama da hare-haren Yan bindiga da satar mutane don karɓar kuɗin fansa, kuma mafi yawan waɗanda ake zargi da aikata wannan laifi duk Fulani ne.

 

Wannan, da ma wasu labarai a biyo mu a shafin www.arewanews.org.ng

Post a Comment

0 Comments