Talla

Al'umma sun gudanar da Addu'o'in zaman Lafiya a Jihar Zamfara

11 Oktoba, 2021
ZAMFARA, NIJERIYA — Wasu mazauna Jihar Zamfara sun gudanar da addu’ar zaman lafiya kan matsalar tsaro da ke ƙara ƙamari a Jihar.
 
Masu addu'ar waɗanda da yawansu ba ƴan asalin Jihar ta Zamfara ba ne sun kuma buƙaci gwamnatin tarayyar Nijeriya ta samar da isassun kayan aiki ga jami'an tsaro da ke yaƙi da ƴan fashi da masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.

Wasu daga cikin waɗanda suka halarci zaman addu’ar sun bayyana cewa a shekaru da suka yi a Jihar ta Zamfara, ba su taɓa fuskantar matsalar rashin tsaro kamar na wannan lokacin ba.

Don haka, ya zama wajibi su yi addau’ar neman zaman lafiya a inda suke rayuwa da ma dukkan Nijeriya baki ɗaya.

An samu jerin hare-haren ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, na baya-bayan nan shi ne sace ɗaliban makarantar sakandaren gwamnati a ƙaramar hukumar Maradun.

Wasu majiyoyi daga ƙauyen Kaya sun bayyana cewa maharan masu yawan gaske sun kutsa cikin makarantar ne a ranar 1 ga watan Satumba kuma suka yi awon gaba da ɗaliban zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.

Sace ɗaliban na Kaya shi ne hari na uku da aka kai kan makarantu a Jihar Zamfara.

Yawan hare-haren ya sa gwamnati ta ɗauki tsauraran matakan yaƙi da ƴan ta da ƙayar baya a jihar kamar rufe kasuwanni da layukan sadarwa.

Garuruwan Katsina da Zamfara da Sokoto da Kaduna dai na fama da tashe-tashen hankulla da satar mutane don karɓar kuɗin fansa.

Ko baya-bayan nan sai da aka datse layukan sada zumunta don a samu damar kawar da matsalar rashin tsaro a Jihohin.

Wannan, dama wasu labarai, ku biyo mu a shafin www.arewanews.org.ng

Post a Comment

0 Comments