Talla

Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari: Ƴan Fashi Na Neman A Basu Abinci Maimakon Kuɗin Fansa

20 Oktoba, 2021 
KADUNA, NIJERIYA - Sarkin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna a Arewacin Nijeriya ya ce, sun ga amfanin matakan da Gwamnatin Jihar ke ɗauka da niyar daƙile ayyukan 'yan bindigan daji masu garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa.

Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II ya ƙara da cewa, matakan sun hana 'yan bindigar samun damarmaki, abin da ya sa yanzu suke neman abinci daga wajen mutanen da suka sace maimakon kuɗin fansa.

Sarkin ya bayyana hakan ne ranar Laraba a wajen taron ƙaddamar da rahoto kan matsalar tsaro da Ma'aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar ta gabatar wa Gwamna Nasir El-Rufai.

Ya ce,
"Mun nuna cewa matakan da gwamnati ta ɗauka na toshe layukan salula da hana hawan mashin da hana sayar da man fetur a ko'ina ya yi amfani ƙwarai da gaske domin mun gani a wajenmu kuma muna da labarin sauran wurare".

Ya ƙara da cewa,
"Waɗannan matakai sun takura su ta yadda idan suka saci mutane saidai su ce a ba su abinci ba kuɗi ba. Muna goyon bayan gwamnati kuma muna addu'ar Allah ya kawo ƙarshen wannan abu."

Rahoton ya duba rikice-rikicen da suka faru na 'yan fashin daji da ƙabilanci daga ɗaya ga watan Yuli zuwa talatin ga Satumba shekara ta dubu biyu da shirin da ɗaya.

Mutum 343 aka kashe sannan aka sace 830 tare da jikkata 210 jumilla sakamakon tashe-tashen hankalin.

Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren ƴan bindiga waɗanda ke satar mutane don karɓar kuɗin fansa.

Post a Comment

0 Comments