Talla

Alhaji Salisu Mamman CONTINENTAL: Mun Gani A Ƙasa A Hukumar KASROMA

19 Oktoba, 2021



KATSINA, NIJERIYA - A ranar 18 ga watan Oktoba ne na shekarar 2021 wata Kungiya mai zaman kanta da ake kira "Mun Gani A Kasa" ta shirya walimar cikar shekaru biyu da jagoranci injiniya Surajo Yazid Abukur a hukumar KASROMA tare da taya sabbin zababbun Shugabanin Jam'iyyar APC murnar rantsar da su.

A wajen taron an yi hudubobi ga Shugabanin Jam'iyyar da kuma shugaban hukumar na KASROMA. sakataren wannan kungiya ya bayya na irin yadda kungiyar ta samo asali da kuma muhimman ayyukan da kungiyar ta wanzar daga kafa ta zuwa yau.

Shima Sakataren Jam'iyyar APC na jiha Malam Shitu S Shitu yayi jawabin godiya a madadin zababbun Shugabanin Jam'iyyar tare da Jan hankalin mutane wajen yin abin da ya dace in an basu jagoranci Kamar yadda Injiniya Surajo Yazid Abukur ke kamantawa.

A nasa jawabin shugaban rukunin kamfanonin Continental Alhaji Salisu Mamman Continental ya bayyana cewa duk wanda ke jihar Katsina a bangaren hukumar KASROMA ya Gani a Kasa ba labari ba na irin ayyukan da hukumar ta shimfida.

Da yake jawabin godiya shugaban Jam'iyyar ya bayyana makasudin shirya walimar da kuma irin nasarorin da ya samu a cikin shekaru biyu da yayi a bisa Jagorancin hukumar KASROMA tare da kawo misalin wasu ayyukan da hukumar ta aiwatar a cikin shekaru biyu na jagorancinsa.

Walimar ta samu halartar mamyan mutane mabambanta da suka hada da shugaban Jam'iyyar APC na jiha Alhaji Sani Ahmad Aliyu Daura da Sakataren Jam'iyyar Malam Shitu S Shitu da Danmajalissa mai wakiltar karamar hukumar Rimi hon. Abubakar Suleiman Korau da mai ba gwamna shawara bangaren siyasa Hon. Kabir Shu'aibu da tsohon Danmajaly mai wakiltar Rimi Hon. Nasiru Ala Iyatawa da sauran su dama.
An tashi taron lami lafiya bayan an ci an sha.

Post a Comment

0 Comments