Talla

Adabin Bariki (Sabo Da Maza)

© Bello Hamisu Ida



Sun dawo daga coci da marece, Magajiya ta kira kowane yaro ta sanya shi irin aikin da zai yi daidai da ƙarfinsa.

Bashir dai ɗibar ruwa ta sanya shi. Ya ci gaba da jido ruwan kamar babu gobe. Gab da magariba ta tsauna kayan abinci suka nufi kasuwar.

Wannan karon ita da kan ta take tura kurar, wani almajiri da ta samo cikin gari ya ke taimaka mata, a haka har suka shiga kasuwar.

Kasuwa ce  babba da ake sayar da abubuwan sharholiya da more rayuwa,

‘Tun daga giyar gida data waje’

Irinsu;

‘shahararriyar giyar Star, giyar whisky, giyar Martini Rose, giyar French Syrup wace ake kawowa daga ƙasar Faransa’,

‘Giyar black doctor, da wace ake wa laƙani da jar giya’.

Ana sayar da burkutu a cikin kasuwar, burkutu irin wace ake sarrafawa da gero ko dawa, ko ruwan kwakwa, ko alkama, ko abarba.

Akwai rumfuna da wasu tsaffi suke sarrafa burkutun,

‘Bayan sun tsuma hatsi na tsawon kwana uku har sai ya fara tsiro’,

‘Akwai wani ɗan ƙaramin fili kusa da rumfarsu sai su barbaza hatsin yadda zai ɗan sha iska’,

‘Sannan su kwashe, su yi ta murzar hatsin har sai ya haɗe ya cure waje ɗaya’,

‘A gefen rumfarsu, akwai wasu manyan tukwane inda suke dafa hatsin har sai ya tafu ya zama burkutu’.

Masu kuɗi, talaka, yara, manya, tsaffi, likitoci, direbobi, ‘yan kasuwa, maza da mata duk suna shan burkutu bisa al’ada a garin Jos’.

        Kowane mashayin burkutu akwai dalilin da yasa yake shan ta,

‘Wasu don magani’,

‘Wasu don su samu ƙarfin jikinsu’,

Wasu don su samu damar yin zurfin tunani’,

Wasu don su samu ƙarfi wajen biya wa iyalansu buƙatarsu’,

‘Mafi yawan kaso suna shan burkutu don su yi maye’.

A cikin kasuwar babu abinda ake ciniki in ka ɗauke abinci irin burkutu.

Sunan burkutu yana da yawa, a kan kira ta da:

Ogogoro, ko Pito, ko Adoyo, ko Omi wara, ko Wuru, ko Kai-kai, ko Agbakara’.

        Akwai rumfunan sayar da abinci, waɗanda takwarorin Magajiya suka buɗe, amma dai ita ce shugabar mata a duk faɗin kasuwar,

‘Shi yasa ma ake ce mata Magajiya’.

Ana sayar da nama kala-kala a cikin kasuwar, kamar:

‘Naman rago, ko naman akuya, ko na bunsuru da naman shanu’.

Ana sayar da naman dabbobin daji (bush meat),

‘Kamar naman alade ko kare’.

‘Akwai masu gasa naman’,

‘Wasu kuwa sai su soya ko su yi farfesu’,

Kwatankwacin yadda mai saye yake sha’awa.

Duk a cikin kasuwar akwai rumfunan yin caca da karta. Mafi yawan masu sayar da abubuwan more rayuwa a cikin kasuwar ‘yanmata ne, wasu kuwa manyan mata ne masu sauran ƙarfi irin su Magajiya.

‘Bayan su akwai ‘yanmata ‘yan shila waɗanda suka ƙara haska kasuwar da ƙamshin budurcinsu’.

Waɗannan ‘yan mata basu da wani aiki, sai in wani ya taya, su bishi gidansa don ɗebe wa juna kewa.

Lokacin da wasu ke cin nama, ko shan gida, ko burkutu, wasu na lale katin caca, wasu kuwa suna sharholiyarsu da ‘yan mata masu jini a jika, ko ‘yan damai-damai, daidai kuɗinka, daidai shagalinka.

Tun daga farkon shigowa kasuwar kuwa, samari, matasa, dattijai da tsaffi suke zaulayarta.

Wasu su kalli mazaunanta su tuntsure da dariya, wasu kuma yanayin tafiyarta suke kwaikwaya.

Wani tsohon Najaddu ya taso daga nesa, sannan ya biyo bayan Magajiya ya ce,

        “Ke magajiya, abubuwan nan har yanzu dai da sauransu”

        Ta kaɗa su, cikin sha’awa da jin daɗi tare da jan hankalin mazan da ke wajen ta ci gaba da rausaya, sannan ta kalli tsohon ta ce,

        “Baba yaro ma albarka, balle kai da babu haƙora, ina abun cin goron?”

        Najaddu ya tuntsure da dariya, har da buga ƙafa sannan ya ce,

        “Ko babu haƙora ai baba tsoho yana da magogin goro”,

Ya ja numfashi ya ce,

“A jaraba bashi, aga yadda baba zai yi sukuwa bisa dokin sarki”

        Daga haka dai bata sake kula shi ba, suka shiga kasuwar, sannan suka sauke kayan dake tsaune a jikin kurar.

Suna gama sauke kaya, ta sanya Bashir shara, shi kuwa hankalinsa na wajen Blessing, yana ta so ya kamala sharar su tafi su yi wasa, kafin duhu ya mamaye sararin samaniya.

Lokacin da yake sharar ya hangi wannan sheɗanin Najaddu ya kama hannun Blessing sun shige wani lungu.

Daga nan bai sake ganinta ba. Sai can wajen ƙarfe goma sha biyu, sannan ya ganta ta nufi hanyar gida, tana tafe tana cin biskit, ga wata alewa a hannunta. Ya bi bayanta da gudu yana kiran sunanta.

Za a ci gaba...

 


Post a Comment

0 Comments