Talla

15 Janairu: Yadda aka kashe Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto (Kashi na ɗaya)

 Daga littafin: IN ZA AKA FAƊI, FAƊI GASKIYA na David Muffett



ABUJA, NIJERIYA Har zuwa ranar mai kamar ta yau ba a samu cikakken bayani a rubuce dangane da abubuwan da suka auku da asussubahin ranar 15 ga Janiaru ba.

Bayanai da aka samu ta hanar gwamnati suna cike da gibai. Mutum zai iya gane dalili saboda al’amarin yana da rassa da dama; kuma da abubuwan da suka fara fitowa fili sai aka fahimci akwai hannun mana-manyan mutane cikin lamarin; ko kuma in mutum ya duba abubuwan da suka auku kafin wannan lokacin sai ya kasa gane shin wane ne mai laifi kuma wake da gaskiya?

Bayan haka, akwai hanyar mafi sauƙi in abu irin wannan ya auku: shi ne a yi rufa-rufa, in ya so a hankali sai a mance da shi, irin wannan abu yana daga cikin aibobin da suka dami Yan Nijeriya tun ma kafin samun ‘Yancin-kai lokacin da mulkin Turawa ya fara yin sako-sako. Saidai, ina! Abu ne mawuyaci a ce za a iya danne irin wannan abu da marubucin wannan littafin yake ƙoƙarin bayyanawa.

Haka kuma, bayanai da aka samu ba a hanyar gwamanti ba, in mutum ya fara bin diddiginsu sai ya taras ba su da makama. Duk da haka nan gaba za a riƙa ambaton irin waɗannan labarai. Wasu daga cikinsu sun fito ne daga irin mutanen da aka yi abin a idonsu; wani lokaci ma da hannunsu a ciki, amma har yanzu ba a daina yin tsokaci kan waɗannan labaru ba.

Abu ne mawuyacin gaske mutum ya sami tsantsar gaskiyar abin da ya auku, saboda haka kada a ɗauka cewa abin da marubucin wannan littafi ya faɗi shi ne tabbas.

Amma duk da haka dangane da muhimman kashe-kashe da aka ba da labari (kamar na su Firayin Minista da Firimiyan Jihar Arewa, da na Jihar Yamma da kuma na Ministan Kuɗi) da kuma labarin manyan hafsoshin Soja da aka kashe; dangane da waɗannan duk an dogara ne da abin da waɗanda aka yi abin a idonsu suka faɗa.

Marubucin wannan littafi ya sami waɗannan bayanan ne ta hanyar gaya masa da suka yi su-da-shi ko kuma su gaya wa wani kuma wani ya gaya masa. Ta wannan ɓangaren ana iya kiransa ji-ta-ji-ta ko da yake mutum ɗaya ne kurum tsakaninsu.

Zargin da ake yi na ƙin yarda da ji-ta-ji-ta a fanin shari'a ya fara samun karɓuwa a ƙasar Ingila. Yanzu ma an fara karɓar shaidar ji-ta-ji-ta ta a kotunan Ingila. Na tabbata nan ba da jimawa ba za fara karɓar irin wannan shaidar hatta a shari’o’in da ake ɗaukan manyan uƙubobi.

Saboda haka akasin abin da aka saba a sha’anin shari’a, za a iya yarda da abin da aka ji, kuma in ana binciken kashe-kashe musamman irin na juyin mulki, abu ne mawuyaci ƙwarai a ce sam ba za a yi amfani da ji-ta-ji-ta ba, musamman saboda an kashe yawancin waɗanda aka yi abin a idonsu.

Duk da haka a muhimmin wuri ɗaya ne kurum aka yi amfani da labarin ji-ta-ji-ta. A duk sauran wuraren sai da marubucin wannan littafi ya yi ƙoƙarin saduwa da mutanen da aka ce sun yi wata magana don ya ji daga bakinsu. Wurin ɗayan kurum da ba a ayi haka ba shi ne inda Okafor ya ce ya sami nasa labarin.

Abin da shi marubucin ya faɗi, da kuma abubuwan da masu bashi labari suka faɗi (waɗanda a kai ne ya gina labarinsa).

Mafi yawancin abin da marubucin ya ce an gaya masa, ya fassara su ne daga maganganun da ya kwasa a rikoda tsakanin watan Agusta da Satumba, ko kuma a watan Yuni na 1969 lokacin da ya ziyarci Nijeriya. Kaset-kaset na waɗannan maganganun har yanzu suna hannun marubucin, amma a nan gaba zai kai su wurin ajiye kayan tarihin mulkin mallaka da ke Jami’ar Oxford ko kuma wani wuri makamancin wannan. An bayyana a fili duk inda aka yi wannan fassara kuma duk wuraren da ba irin wannan fassara aka yi ba, to, an yi bayanin yanda aka yi aka samo labarin.

Watakila mafi muhimmancin labarin da ya danganci wannan sashe shi ne mutumin da ya ba Okafor bayani. Da ake wannan labari ana iya cewa ji-ta-ji-ta ne, marubucin wannan littafi ya yi ƙoƙarin gwargwada shi da sauran labarai da aka samu daga wasu wurare don ganin inda ya yi kwana da inda ya miƙe. Wannan ita ce hanyar miƙaƙƙiya ta gaskiyar labari. An ɗauka cewa in dai wasu sassa na labarai sun zama ɗaya ana iya cewa gaskiya ne ko da ba a san yadda za ayi a tabbatar da gaskiyarsu ba. Wannan hanyar ce da aka yi amfani da ita tun-tuni a fanin yin shari’a inda aka haƙiƙance cewa, inda kowa ya ce, “a’a” sai kurum a ɗauka “a’a” ne. saboda haka a nan in sun haɗu sai a kyale shi a haka, in basu haɗu ba sai a bincika.

Duk irin layin da aka ɗora a kan kowane ɗaya daga cikin abubuwan da suka auku kamar yadda aka faɗi, akwai wani guda ɗaya da aka manta a lura da shi. Ko kaɗan ba zai yiwu ace masu ba da labarun sun auna sun tattauna a tsakaninsu ba, saidai wataƙila su Madawakin Bauchi da Kafan; da kuma Kadiri na Raɓah da Salloma. Amma babu shakka ba zai yiwu a ce sauran sun taɓa jin labarin mutumin da ya gaya wa Okafor nasa labarin ba. Kuma dangane da labarin da Chukuma Nzeoguwu ya bayar a wata hira da yan jaridu suka yi da shi, ba a kawo shi a ƙarin bayani ba. Amma duk inda aka yi amfani da irin wannan labarin, an bayyana wurin da aka samo shi.

Akwai wata matsala mai ɗan ta da hankali da za ta bayyana ga marubucin wannan labarai, musamman dangane da kisan Firayim Minista da Birgedia Maimalari. Gwanatin Nijeriya ce kurum ke riƙe da wasu bayanai waɗanda za su ƙaryata wannan labarai ko kuma su tabbatar da shi. Ina fatan gwamnatin za ta yi hakan, domin kuwa ta wannan hanyar ce kurum za a ƙara fahimtar yawancin abubuwan da suka gudana.

Wani lokaci can baya kafin sallar kirismeti, Manjo Patrick Chukuma Kaduna Nzeogwu wanda shi ne babban malami a Makarantar Koyon aikin soja na Nijeriya da ke Kaduna, ya ƙarfafa yin aikace-aikacen koyar da sojoji cikin dare. Wannan ya sa mutane da suke zaune a wuraren da ke kusa da Nasarawa suka saba da ganin walƙiya da kuma jin ƙararrakin bindigogi.

Arewa News ce ta ɗauki ɗawainiyar sake yin kofin littafin da wallafawa a shafinta don sanin Tarihin Ƙasar Nijeriya.

www.arewanews.org.ng

Post a Comment

0 Comments